al-mustapha-zai-fasa-kwai

Tsohon dogarin shugaban kasa marigayi Sani Abacha wato Major Hamza Al-Mustapha ya bayyana cewa zancen kudin da ake cewa uban gidansa ya sata gami da boye su a kasar waje ba gaskiya bane, hasali ma taimaka wa kasar yayi.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da yan jarida da yayi jiya a Lagos inda ya bayyana cewa Abacha ya boye wannan kudade ne don tunanin cewa akwai kasashen da ke son sanyawa Nigeria takunkumi.

Ya kara da cewa sai da akayi meeting da manya-manyan jami’an gwamnati a Abuja inda suka abince da a aje kudaden don kare kai idan takunkumin yazo.

Al-mustapha ya bayyana wa yan jarida cewa akwai wasu makiyan Gen. Abacha wanda suka hada kai da wasu kasashen ketare wajen ganin sun kifar da gwamnatinsa amma duk sai basu ci riba ba inda dai a karshe sukayi nasarar kawar dashi.

Almustapha yace: “Kamar yadda na bayyana a baya cewar, wadanda sukayi sanadiyyar mutuwar Abiola to sune suke da alhakin kisan Abacha. Da zarar na gama da cases din dake gabana a kotu, to zan bayyana wa al’umma gaba daya abinda ya faru dangane da mutuwar Abacha.”

Sannan ya bayyana shugaba Buhari a matsayin shugaba na gari mai gaskiya kuma mai adalci haka zalika mai kishin kasa. Inda ya bayyana cewa wadannan halayen ne ma suka duba wajen bawa Buhari shugaban PTF(petroleum Trust Fund).

Tura ma Abokanka don suma su karu.. Zaka iya turawa ta facebook, twitter ko whatsapp da sauran su…