Kannywood bokoharam movie
Photo: premiumtimesng

Abu Hassan wani sabon wasan kwaikwayo ne da masana’antar shirya fina-finan Hausa ta shirya don wayar da kan mutane kan irin barnar da yan ta’adda ke yi musamman kan salon boko haram da kuma yadda aka yakesu.

Jami’in shirin kuma babban jarumi a harkar wasan Hausa wato Zaharaddeen Sani ya bayyana dalilansa na shirya wannan wasan kwaikwayo duba da irin hadarurrukan da wasu ke ganin film din na tattare dasu.

A hirar sa da jaridar premiumtimes, jarumin ya bayyana cewar matsayinshi na dan kasa na gari yaga ya dace ya shirya wannan wasan kwaikwayo don wayar da jama’a kan irin ta’addanci da kuma irin barnar da yan tada kayar baya keyi a cikin al’umma.

Ya bayyana cewar sai da yaje hedikwatar jami’an yan sanda na farin kaya da kuma hukumar tace fina-finai don amsa wasu tambayoyi dangane da film din kafin daga bisani a bashi umarnin fitar da film din.

Jarumi Adam A Zango da kuma shi Zaharaddeen Sani ne manyan taurari a cikin wannan wasan kwaikwayon a matsayin jami’an tsaro masu kishin kasa don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da Tanimu Akawu wanda yake a mazaunin Abu Hassan wanda shine shugaban kungiyar yan ta’adda dake garkuwa gami da kisan fararen hula ya zuwa jami’an tsaro.

Owner Movies ne suka kawo muku shirin. Film din nanan zuwa gareku a watan April mai kamawa.

Ku kalli tallar wasan kwaikwayon ta link din youtube dake kasa