munyi nazari kan abubuwa biyar da suka fi tayar
da kura a a masana’antar, wacce ke da farin jini
sosai:

1. Auren jinsi
Wani abu da ya jan hankalin jamaa sosai kuma ya tayar da jijiyar wuya shi ne zargi hada auren jinsi da aka yi wa wasu taurarin Kannywood hudu da yi a
birnin Kano a watan Afrilun shekarar 2007.

Lamarin da ya sa suka shiga buya, bayan
hukumar shari’a ta Hizba ta samu labarin sannan ta shiga nemansu.

Ko da yake a wata hira daakayi da Aunty Maiduguri wadda aka zarga da hada auren ta musanta zargin.

2. Fim din batsa ko Blue Film

‘Yan Kannywood sun samu kansu a tsaka mai
wuya a watan Agustan shekarar ta 2007, inda
aka zargi Maryam Usman Hiyana da Saurayinta Usman Bobo da yin fim din batsa.
Fim din da aka yita yadawa kuma ya janyo
matukar suka ga masu harkar fina-finan.
Fim din batsan ne kuma ya kawo karshen fitowar Hiyana a fina-finan Hausa bayan an kore ta.

3. Zargin luwadi

A watan Agustan 2016 ne kuma zargin luwadi ya dabaibayi masana’antar.

Lamarin da ya kai har fitaccen jarumin nan kuma mawaki, Adam A Zango, rantsuwa da alkur’ani mai tsarki yana kare kansa. Batun ya taso ne bayan da aka zargi wasu daga
cikin masu harkar fimdin da cewa ‘yan luwadi ne.
Sai dai a wannan karon babu wani da aka
fayyace sunansa.

4. Gina alkaryar fim

Batun gina alkaryar fim a jihar Kano wanda
gwamnatin tarayyar ta so gudabarwa ya tayar da jijiyoyin wuya a baya a watan Julin bana.

Malaman addini da jama’a ne suka nuna adawa da shirin, suna masu cewa zai daurewa badala da shashanci gindi a jihar.
Sun zargi ‘yan fim da cewa mutane marasa
kamala da ke yada batsa.
Sai dai masu shirya fim din sun ce ba haka
lamarin ya ke ba, kuma mummunar fahimta ake
yi musu.

5. Rahama Sadau ta rungumi Classiq

Batun rungumar mawakin nan, Classiq da
Rahama Sadau ta yi shi ne abu na baya-bayan nan da ke jan hankali masu bin al’amuran Kannywood da ma jama’ar gari.

Yayin da wasu ke sukarta kuma kungiyar shirya fina-finan Hausa ta kore ta, Rahama ta nemi gafara tare da kokarin fahimtar da mutane cewa duk abin da ta yi a wakar aikinta ne ya bukaci haka ba son rai ba.

Kungiyar ta ce ‘yar wasan ta yi karan-tsaye ga
ka’idojin kyawawan dabi’un da Kannywood ta
ginu a kansu, lamarin da ta ce shugabannin
harkar ba za su lamunce da shi ba.

Sai dai wasu na korafin cewa akwai wasu ‘yan
wasan da a cewarsu suka yi abin da ya fi na
Rahama, kuma ba a dauki mataki a kansu ba.
Masu korafin na ganin an kawar da kai ga abin da taurarin fina-finai kamar su Ali Nuhu da Sani
Danja da kuma Adam A Zango ke yi a wasu fina-
finan ko wakoki.

Ads