Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Fitaccen jarumin Kannywood Adamu Abdullahi Zango ya bayyana ko su waye ya dauka makiya da kuma dalilin da yasa yake musu habaici.

A hirar shi da Nasidi Adamu Yahaya, an tambayi Adam Zango akan dalilin da ya sa yake yawan yi wa makiyansa habaici a shafukan sada zumunta, sai ya ce yawan makiyan da yake da su ne ya sa yake yawan wallafa sakon habaice-habaice a shafinsa na Instagram.

Jarumin ya ce abin da ya dauka makiyi shi ne duk mutumin da ba ya bukatar ya ga “ci gabanka ko kuma idan ka yi wani abin burgewa, amma shi bai ga hakan ba, to makiyinka ne.”

“Ko kuma mutumin da idan wani abu ya zo maka na karuwa kamar karramawa ko taron kalankuwa ko na biki, amma sai ya ce kar a bai wa wane, gara a bai wa wane, to makiyinka ne.

“Dole ne a masana’antarmu sai ka samu makiya, wasu na jikinka ne, ko daraktoci, ko jarumai ko furoduoshi ko ‘yan wasa.

“Dan Adam bai son kishiya, duk wanda ya ga wani yana daga wa ko yana neman ya wuce shi a daukaka to zai ji haushi,” a cewar Adamu.

Jarumin ya ci gaba da cewa idan ya yi maganar makiya to ba da mutum daya ko biyu yake ba, yana magana ne kan mutane da dama da suke nuna masa irin wadancan halayyar da ya ambata.

Wanda ya tsargu da shi ake.
Jarumin ya ce idan mutum ya yi habaici to duk wanda ya tsargu, tabbas yana cikin wadanda ya rubuta sakon saboda su.

“Sannan akwai masu bin mu wato fans, amma kuma makiya ne.
Za ka yi abin da ba wanda ya taba yi a duniya, amma sai su ce karya ne kwaikwayon wani ka yi.

“Don haka na kan yi wasu abubuwan ne don na burge masoyana, a hannu guda kuma na aikewa makiyana sako a fakaice cewa na san irin kiyayyar da suke min,” in ji Adamu Zango.

BBChausa.


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •