Shidai wannan hoto da kuke gani na jarumi Adam A Zango ya dora shi a shafinsa na Facebook inda ya rubuta cewa ya koma gona, kasantuwar noma shine tushen arziki.

Adam A Zango ya koma gona

Jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan wannan post na Facebook da shi jarumin yayi inda wasu ke ganin bai kamata a ce jarumin na zuwa gona ba, a yayin da wasu kuma suke ganin hakan yayi daidai.

Da alamu dai jarumin ya dora wannan hoto ne kawai don jin ta bakin jama’a wanda kuma ya samu hakan.

Jaruman fina-finai sukan dora hotuna makamantan wannan don jin ta bakin masoyansu, idan baku manta ba a jiya ma munyi wani post akan wani hoto da jarumi Ali Nuhu ya dora akan shafinsa na Facebook inda a cikin hoton anga yan sanda tare da Ali Nuhun sannan da kuma wasu manyan makamai a gabansu wanda hakan ke gwada kamar an kama shi da su ne ( Yan Sanda Sun Kama Bindigogi A Gidan Ali Nuhu ) , sai dai hakan fa ta faru ne a cikin wani film da suka haska.

Ads