Shahararren jarumin wasan Hausa Adamu Abdullahi wato Adam A Zango ya sanya gasar kudi akan sabon fim dinshi mai taken “Gwaska Returns” wanda za’a fara haska shi a cinema a wannan watan da muke ciki.

Ita dai wannan gasa zata fi cancanta ga masu yin comedy video ko makamancin hakan. Sannan gasar zata dauki tsawon sati daya ne a nayi wato daga yau 9th January zuwa 16th January 2018, inda daga karshe za’a zabi wanda ya cinye gasar sannan a bashi kyautar shi ta tsabar kudi har naira dubu hamsin (50,000).

Wannan ba shine karo na farko da jarumin kan sanya irin wannan gasa ba domin ko a can baya ya sanya gasa da dama gami da bada kyautuka wa wadanda suka yi nasara musamman akan shi wannan film din na “Gwaska Returns”.

Yadda gasar take

Kamar dai yadda aka saba. Zaka dauki video sai kayi upload nasa tare da hashtag na #gwaskayadawo.

Video da zaka shine kayi shiga irin ta gwaska sai ka cece wanda ake kokarin zalunta na kamar tsawon minti daya sannan sai kayi uploading zuwa account dinka na instagram tare da sanya hashtag din #gwaskayadawo.

Za’a fara haska wannan film a katafaren dakin kallo dake ciki shoprite zoo road Kano a ranar 19 ga watan January din nan da muke ciki kamar yadda jarumin ya sanar a shafinsa na instagram.

Allah ya bada sa’a.

Ads