Barkanku da wannan lokaci maziyarta shafin fasaha na arewamobile. A yau ina dauke da bayani akan yadda zaka more garabasar data ta browsing har 6gb akan Naira 1500 kacal.

A dazu ne kamfanin airtel suka turo min da sakon wannan garabasa da suka yiwa lakabi da 100% bonus data wacce take iya yin amfani akan kowacce irin waya ko kwamfuta. Haka zalika wannan data din za’a iya amfani da ita akan ko wanne irin application; na waya ko na kwafuta.

Ita dai wannan data za’a iya yin kwana talatin ana amfani da ita, ma’ana tsawon zangon data din shine kwana 30 (wata 1).

Hakikanin ainihin yawan wannan data shine 3gb amma sai kamfanin airtel ya yanke shawarar bada wannan garabasa ta dan gajeren lokaci, saboda haka ba dadewa zasu yi suna bada wannan garabasar ba.
Domin more wannan garabasar data bonus sai kawai ka sanya katin N1500 akan layinka na airtel sannan sai ka dannna *440*161# kamar yadda yake a hoton nan dake kasa

Tura wa abokai….