Share this on:
 • 27
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  27
  Shares


Uwar gidan shugaban kasa Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta karrama jarumi Ali Nuhu tare da wasu tare da wasu manyan jarumai da masu ruwa da tsaki a kannywood a fadar gwamnati dake Abuja.

Wannan dai shine karo na biyu da matar shugaban kasan ke karrama yan wasan Hausa tare da mawaka bisa irin gudummawar da suka ba kuma suke cigaba da baiwa mai gidanta don ganin ya cimma nasara.

Daga cikin wadanda aka karrama akwai, Bello Muhammad Bello, General BMB, Nazir Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Waka, Ibrahim MaiShinku, Abdulamart Maiikwashewa, Falalu A. Dorayi dadai sauransu.

Masana’antar kannywood dai ta rabu gida biyu dangane da yantakar shugabanci kasa da muke dasu, inda wasu suka zabi subi bayan turakin Adamawa, a yayin da wasu kuma suka zabi su cigaba da tafiya da shugaba Muhammadu Buhari.


Share this on:
 • 27
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  27
  Shares