Bayanai na nuni da cewa akwai yiwuwar jarumar nan ta wasan kwaikwayo na kannywood da kungiyar ta sallama a kwanakin baya wato Rahama sadau zata koma masana’antar masu shirya fina-finan kasar amurka wato Hollywood.

Hakan ya biyo bayan gayyata da wasu fitattun jaruma guda biyu suka yi mata da cewar tazo suna maraba da ita a Hollywood don ta rinka yin wasan kwaikwayo a tare dasu.

Idan ba’a mance ba a kwanakin bayane hukumar shirya fina-finai ta kannywood MOPPAN ta kori Rahama sadau daga masana’antar film

Shahararren mawakin nan kuma jarumi a harkar film mai suna Akon ne ya fara rubuto mata katin gayyata a shafinsa na twitter inda ya bayyana cewar kamata yayi a rika karfafa wa mata masu harkar film gwiwa ba a dakile su ba, sannan kuma ya bukaci da tazo domin ta fara harkar film dasu a can amurkan.

Wani fittacen jarumin na Hollywood Jetta Amata wanda asalin dan Nigeria ne shima ya bukaci ganin rahama sadau din ta shigo harkar wasan kwaikwayo na Hollywood. Shima dai yayi wannan rubutu ne ta shafinsa na twitter.

Jarumar ta yaba da wannan gayyata da aka yi mata inda ta nuna matukar farin cikinta dangane da hakan a shafinta na twitter.

Jama’a dai suna ta tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan abu da ake ganin cewar jarumar ta samu cigaba inda wasu ke ganin ba cigaba bane a gareta duba da irin bambanci na al’ada da kuma addini na wadanda zata yi harkar da su a Hollywood din..

tura wa abokai…