Kakakin rundunar yan sanda na kasa, sifeto janar Solomon Arase ya bada umarnin cafke duk wani wanda aka kama yana sana’ar bumburutu a ko inane a Najeriya.

kakakin-yan-sanda

Kakakin ya bayyana cewa duk wanda aka kama yana siyar da mai ko kuma yana dauke dashi a cikin jarka ko wani abu makamancin hakan to lallai zai dandana kudarsa..

Yayi wannan jawabin ne ta bakin mai magana da yawunsa wata Olabisi Kolawole inda ya bayyana cewa masu sayar damai ta bayan fage na karo jawo wasu karin wahalhalun da yan Najeriya ke sha.

Mr Arase dai ya kara da cewar irin wannan mai da ake sayarwa a jarkoki kan haifar da gobara wanda hakan ke jawo asarar dukiya ta mutanen da basu jiba basu gani ba..

Ya gargadi masu bada mai a gidajen mai dasu guji sayar da mai wa yan bumburutun domin duk wanda aka kama yana siye ko yana siyarwa to tabbas zai fuskanci fushin hukuma..

Ko menene ra’ayinku dangane da hakan??? Ku tura wannan sakon ya zuwa shafukan sadarwa na facebook,twitter, whatsapp da sauransu….