Share this on:
 • 54
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  54
  Shares

A yammacin jiya asabar ne dai hadaddiyar kungiyar tace fina-finan Hausa ta MOPPAN da sauran kungiyoyin shirya fina-finai suka samu nasarar sasanta rikicin da ya barke tsakanin jarumai guda biyu; wato jarumi Adam A Zango da kuma Ali Nuhu.

Wannan matsaya dai tana zuwa ne a daidai lokacin da jaruman ke shirin haduwa a kotu ranar litinin din nan mai zuwa bisa karar da daya daga cikin su yayi kan cewar an yi masa sharri gami da bata suna.

Salisu Mu’azu Jos shine wanda ya jagoranci zaman, tare dashi akwai shugaban kwamitin amintattu na MOPPAN, Abdulkareem Mohammed, da kuma shugaban MOPPAN na kasa, Abdullahi Maikano, da kuma wasu manya da tsofaffin yan film kamar su Abdullahi Baba Qarami, Kabir Mai Kaba, Shu’aibu lilisco da dai sauransu.

Daga karshe jarumi Ali nuhu ya bayyane cewar zai janye karar Adam Zango daya shigar gaban kotu..


Share this on:
 • 54
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  54
  Shares