Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Shahararriyar jarumar Bollywood, Deepika Padukone na fuskantar barazana ga rayuwar ta a sakamakon rawar da ta taka a wani sabon fim da bai fito kasuwa ba mai suna Padmavati.

Kungiyoyi masu tsattauran ra’ayin addinin Hindu har ma da ‘yan siyasa mabiya addinin na ganin cewa fim din ya ci masu zarafi ta hanyar nuna wata shahararriyar sarauniyar su a can wani karni a baya wacce suke matukar girmamawa ta na soyayya da wani sarkin musulmi.

Deepika ita ta fito a matsayin sarauniyar a cikin fim din.
Toh sai dai daraktan fim din wanda shi ma ba a barshi ba a barazanar, Sanjay Leela Bhansali ya bayyana cewa sam wannan batu ba haka bane. Ya ce babu inda sarauniyar ta yi soyayya da musulmi a cikin fim din, amma wannan bai hana masu barazanar ci gaba da yin barazanar su ba.

Lamarin dai ya fara ne tun a farkon shekarar nan, bayan da wata kungiyar hindu mai suna Rajput Karni Sena ta fara barazanar kona duk wani gidan sinima da aka nuna fim din a fadin kasar.

Lamarin ya kara kamari bayan da wani shararraen dan siyasa kuma mai magana da yawun jam’iyyar Bharatiya Janata (BJP) Surajpal Amu ya sanar da ladan dala miliyan biyu ( Miliyan 720 a Naira ) ga duk wanda ya gille kan jarumar da darakta Bhansali.

Tuni dai shuwagabancin jam’iyyar ta nisanta kanta daga wannan barazana.

Haka zalika shuwagabanni a jahar Maharashtra wacce ita ce jaha ta biyu a adadin jama’a a kasar ta India suka bayyana yiwuwar hana nuna fim din a jahar, lamarin da zai haifar da gagarumar asara ga mashiryan fim din.

A ranar 1 ga watan Disambar shekarar nan ne aka yi niyyar fara nuna fim din a sinimoni a fadin kasar, amma saboda wannan tashin tashina, an daga ranar har sai baba ta gani.

Tuni dai Deepika ta soke ziyartar wani taron kasuwanci na duniya da zummar kare kanta.

Haka zalika gwamnatin jahar ta ta Karnataka ta shiga lamarin, inda ta yi alkawarin daukan tsattsauran mataki ga dun wanda ya yi yunkurin taba jarumar.

Written by: alummata.com


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •