Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Jaruma Fati Muhammad ta yi wannan bayani ne a wata hirar bidiyo inda ta bayyana dalilin da ya sa auren yan film yake macewa da wuri wanda hakan yasa jama’a ke musu kallon cewa ko su basu son zaman aure ne.

Fati Muhammad

“Shidai Allah shine ya halici aure kuma ya halicci saki. Amma halal din da Allah baya so shine saki, Mutuwar aure. Abinda nake so yan kallo su gane shi mutuwar aure ya zama ruwan dare game duniya, idan gidanku baku sako ba to ku an sako muku. ”

“Amma duniya bata daukar cewa wance bazawara ce a gidan su, sai kaji ance yan film basa zaman aure, wanda kuma abinda ke faruwa mafi yawancin jama’a suna mana auren sha’awa mu kuma bama dubawa.”

“Wani zaizo yai miki karya, wani zai fito miki a mutumin kirki ba tare da ya neme ki da fasikanci ba, kuma zai kashe kudinsa ko nawa ne don ya aureki. Amma da zarar bukatar sa ta biya sai ya sake ki. ”

” Mu bamu ki zaman aure ba, Allah ne ya kaddara mana haka, muma ‘ya’ ya ne haifar mu akai ba wanda ya fado daga sama. Saboda haka ya kamata in mukayi aure a rinka yi mana fatan alkhairi ba fatan sharri ba.”

Jarumar dai bata kara aure ba har yanzu tun bayan mutuwar aurenta na farko da Sani mai iska.
www.arewamobile.com

Amma shin jama’a bakwa tunanin cewa wasu daga cikin yan film din sune ke janyo ma kansu ayi musu auren sha’awa duba da yanda wasu daga cikin su ke yin shigar dake bayyanar da tsiraici?


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •