A wata hira da sashen Hausa na BBC, fitaccen jarumin wasan kwaikwayon Hausa da turanci wanda ake yi wa lakabi da “Sarkin Kannywood” wato jarumi Ali Nuhu ya bayyana cewa shida jarumi Adam A Zango kamar Danjuma ne da Danjummai.

Ya bayyana cewa zaton da mutane suke na cewar suna takon saka tsakanin shi da jarumi Adam A Zango ba haka bane, inda ya bayyana cewar shi da Adam A Zango kamar wa da kanine kuma suna da kyakkyawar alaka a tsakanin su.

“In kuna tsaman Allah da Annabi dakai da mutum dole ne za’a saba za kuma a gyara, sabawar bawai tana nufin wane yana kin wane bane, a’a, sai anyi haka za’a gane me wane yake so in fahimta, me kuma nake so wane ya fahimta, sannan a samu matsaya.”

Wannan hirar dai ta samo asali ne daga tambayar da aka yima jarumin kan lakabin “Sarki” da ake yi masa akan cewar ko yana da waziri, inda ya amsa da cewar shidai abinda ya sani jama’a suna ce mashi sarki, Adam A Zango kuma yarima..

Ads