Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Daya daga cikin fitattun masu shirya fina-finan Hausa a Najeriya ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta kai musu daukin gaggawa domin hana harkar fina-finan na Kannywood durkushewa.

Zaharaddeen Sani ya ce Kannywood ta kama hanyar durkushewa kurmus, kuma tallafin hukumomi ne kawai zai iya tserar da su.

“A yanzu babu riba a harkar fim, asara muke yi… Yawancin jarumai na rige-rigen kafa wasu sana’o’in daban,” in ji shi.

A kwanakin nan dai wasu manyan jaruman Kannywood sun kara bazama wurin fadada hanyoyin samun kudadensu.

Jarumi Ali Nuhu ya bude wani shagon sayar da kaya a Kano, yayin da Sani Danja da Yakubu Muhammad suka bude gidan hoto.

Zaharadden ya ce: “Na samu labarin cewa gwamnati na shirin yin wani abu kan wannan matsalar, amma ina bayar da shawarar cewa ka da a tallafawa tsirarun mutane domin hakan ba zai kawar da matsalar ba sai dai ya azirta wasu ‘yan kalilan”, kamar yadda ya shaida wa Premium Times.

Ya kara da cewa duk lokacin da aka bayar da kudi irin wadannan, “to wasu mutane ne kawai za su wawure domin amfanin kansu”. Sannan ya yi kira da gwamnati da ta gina gidajen kallon fim a arewacin kasar.

Tuni dama jarumai mata kamar Rahama Sadau da Hadiza Gabon suka fara sayar da kayayyakin kwalliya da kuma yin tallace-tallace ga kamfanoni.

Yayin da wasu kuma kamar su Adam A Zango suka kara kaimi a fagen waka da kuma shirya tarukan wakoki musamman a lokutan bukukuwa kamar na sallah da sauransu.

Da ma wasu masu sharhi sun fara alakanta irin wannan fadada harkokin da wasu jaruman ke yi da karancin armashin da fina-finan suke kara yi.

Zaharadden ya ce a yanzu aikinsu shi ne su shirya fim su sayar ga DSTV ko Arewa TV, saboda babu riba.

“Na shirya fim (Abu Hassan) kwanaki, inda na tafka asara saboda na kashe kudade amma na buge da sayar da shi ga DSTV a arha. Wannan shi ne abin da muke yi yanzu,” in ji jarumin, wanda har ila yau ya kware wurin shirya fina-finai.

Masu shirya fim sun dade suna kokawa kan satar fasahar da suka ce ana yi musu.Sannan kuma a yanzu suna fuskantar barazana daga fina-finan China da Amurka da Turkiyya da ake fassara wa zuwa harshen Hausa, kuma ake samunsu a tashoshin tauran da’adam cikin sauki.

-BBCHAUSA


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •