Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Jarumin kannywood Haruna Talle Maifata ya bayyana ra’ayin sa game da yin bikin zagoyowar ranar haihuwa inda ya bayyana cewa baya yi domin baya goyon bayan yahudancin.

Yayi kira ga sauran yan uwan sa dake bikin wannan ranar da su cire shi cikin harkar kana zai bi wajen cire hotunan duk wadanda ya taya su murya a baya daga wayar shi.

Haruna ya wanzar da kanshi daga
sauran abokan aikin shi dake gangami wajen shirya liyafa na murnar zagayowar ranar haihuwar su.

Jarumin wanda ya faye fitowa mukamin mugunta cikin fina-finan hausa ya kora wannan bayani a faifan bidiyo da ya wallafa a shafin sa na Instagram ranar asabar 27 ga wata.

A cewar shi, muhimmin abun da yake tsoro shine haduwar sa da mahalicin sa inda zai bayyana ayyukan alkhairi da ya aikata a duniya da kuma abubuwa da yayi da arzikin da yasa samu.

Shi dai jarumin yace shi dai bai hana mai ra’ayin yin wannan bikin amma shi dai ba zai goyi bayan yin hakan.
Yayi jan kunne kan tsunduma wajen aikata ayyukan alkhairi wadanda zasu taimaki dan Adam a lahira kamar aiwatar da ayyukan sadakatul jariya.

Wannan labarin ya fito bayan kwana biyu da fitacciyar jaruma Nafisa Abdullahi tayi liyafar bikin murnar zagowar ranar haihuwar ta wanda har ta gayyaci yan uwa da abokan huldar ta dake masana’antar Kannywood.

Kwanan baya ma jaruma Haleema Atete ta hada makamancin haka yayin da tayi bikin cika shekara 29 a duniya cikin watan nuwamba na bara.

-Pulse Hausa


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •