hotunan dan kuka a birni

Fitaccen mawaki kuma dan wasan Hausan nan da tauraruwar sa ke haskawa a wannan zamani wato Ado Isa Gwanja ya musanta rade-radin cewar da ake wai yan sanda sun kama shi.

Jita-jitar dai ta kara karfi ne a makon da ya gabata inda aka yi ta yada cewa wai jami’an tsaro na neman jarumin a yayin da wasu ma ke ta yada cewar wai an kama shi.

Sakamakon surutai da naji sunyi yawa ya sanya arewamobile yanke shawarar tuntubar jarumin wato shi Ado Gwanja din don tabbatar da gaskiyar labarin ko akasin hakan inda ya shaida mana cewar wannan zance kanzon kurege ne.

Ya kara da cewar masu yada jita-jitar sun samo ta ne daga cigaban shirin Dan kuka wato Dan kuka a birni inda aka hasko jarumin yana satar kayan jami’an tsaro wanda hakan yasa yan sanda nemansa amma a cikin film din.

Jarumin yayi kira ga jama’a da suyi watsi da jita-jitar da ake ta yadawa…

Ga wasu daga cikin hotunan film din dan kuka a birni

hotunan dan kuka

hotunan dan kuka

hotunan dan kuka

dan kuka a birni pics