A ranar Alhamis 22 ga watan Disamban nan data gabata ne rundunar sojin Nigeria ta samu nasarar kakkabe yan ta’adda na bokoharam daga dajin Sambisa dake jahar borno, inda yan ta’addan da yawa suka rasa rayukansu a yayin da kuma aka sami nasarar cafke wasu da ransu.

Idan baku manta ba munkawo muku rahoton cewa Sojoji Sun Kama Wani Farar Fata A Dajin Sambisa wanda ba’a bayyana ko dan wace kasa bane a lokacin sakamakon bincike da ake gudanarwa akan shi.

Jaridar Dailytrust ta Yau laraba ta ruwaito cewar wannan baturen da sojoji suka kama yayin dauki ba dadi a dajin Sambisa dan kasar Faransa ne wanda ya kasance kwararre a bangaren sarrafa gami da gyara manya-manyan makamai da yan bokoharam ke amfani da su, a yadda jaridar ta samu labari daga majiya mai karfi.

Gwamnati taki bayyana bayanan baturen da aka kama ne saboda halin zamantake wa gami da kuma karin bincike da ake yi don kara tatso bayanai daga gurin shi wanda aka kama din.

“an kama shi ne a kewayen Bama inda yayi alkawarin bayar da bayanai masu mahimmanci ga jami’an tsaro. An gano cewa dan France ne, amma hukumomin tsaro basu so a bayyana hakan saboda hali diplomasiyya da kuma gudun mayar da hannun agogo baya bisa nasarar da aka samu.

Sai dai a yayin da aka tuntubi ofishin jakadancin kasar Faransa dake dake Nigeria ta sakon email don jin ta bakinsu dangane da lamarin basu ce komai ba.

Yan Nigeria dai sun kasa kunne don jin abinda hukumomin tsaron kasar zasu ce dangane dashi wannan farar fata da aka kama..

Tura zuwa abokanenka dake Facebook, Twitter, WhatsApp da sauransu.