BAYANIN AIKIN HAJJI DA UMRAH CIKIN SAUQI NA(2).
**************************************************

-muna cikin Bayanin yadda Ake yin Umrah,Inmunkammala
Bayanin umrah yanzu Zamushiga bayanin Yadda ake Ayikin HAJJI kaistaye Insha Allahu.

-Bayan Kagama Dawafi To Aiki nagaba Cikin Umrah shine :-
Mutum zai tafi wajen Sa’ayi wato (Safa da Marwa)kenan Allahu(SWT) yana cewa:-
Hakika Safa da Marwa suna cikin alamomin wajen bautawa Allah.

Yadda ake yin Sa’ayi (Safa da Marwa) kuwa shi ne, Manzon Allah (SAW) ya fara da Safa kamar yadda Allah (SWT) ya fara ambaton ta a cikin Alkur’ani mai girma don haka zaka hau dutsen Safa sai ka yi kabbara (ALLAHU AKBAR) sau uku, sannan ka ce:

لاَ إِلَـهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، لاَ إِلَـهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ، أَنْـجَزَ وَعْدَهُ، وَنَصَرَ عِنْدَهُ، وَهَزَمَ اْلأَحْزَابَ وَحْدَهُ.

LA’ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LAA SHARIKA LAHUU LAHUL MULKU WALAHUL HAMDU WA HUWA ALAA KULLI SHAI’IN KADIR. LA ILAAHA ILLALLAHU WAHDAH, ANJAZA WA’ADAH WA NASARA ABDAH WAHAZAMAL AHZAABA WAHDAH.

Sannan sai kayi addu’a, haka ka karanta har sau uku(3). Sannan sai ka sauqo zuwa Marwa har sai ka hau wani waje da ake kira (Badanul waadi)dade an yi masa alama da Koran tayel kamar yadda Akabamu labarikenan Don Bantaba zuwa sede malamai suna bamu labarin yadda wajen yake.

To inkaje wajen Saika aikata irin abin da ka aikata a dutsen Safa.
Haka dai za kayi har sau bakwai ka fara da Safa zaka kare da Marwa.
Amma babu laifi ga wanda ya yi Dawafi ya ji ya gaji ya jinkirta yin Sa’ayi zuwa wani lokaci. Ba dole ne sai ya jera shi da yin Dawafi a lokaci daya ba.
Wallahu Aalam.

maza ana so duk lokacin da mutum ya zo wani waje a tsakanin duwatsun biyu ya yi gudu ko sassarfa a cikinsa a duk lokacin da ya zo wajen matukar dai babu cinkoson da zai hana hakan.
Kuma an yi alamar da take nuna farkon wajen da karshensa.

Shi ma Kai-komo tsakanin Safa da Marwa bashi da kebantacciyar addu’a, mutum zai iya yin Karatun Alkur’ani ko addu’ar da ya sauwaka .

Daga nan kuma sai yin
ASKI KO SAISAIYE(saisaiye shine Aski ahausar wasu kenan) ga namiji.
mace kuma ta rage gashin kadan kamar centi mita daya (1cm) TO DAGANAN Umra ta cika kenan.

Amma Yamata Idan Umrar na daf da aikin Hajji to zaifi dacewa ga namiji ya yi Askinshi domin in an kare aikin Hajji za’a sake yi.

To a nan ne mai Tamattu’i zai cire haraminsa kuma ya yi aski wato ya cika Umararsa kenan.

Zamuyi Bayanin TAMATTU’IT agaba domin kagane darasin soasai.
Kuma a duk lokacin da mutum ya je Makka domin yin Umra to daga nan ya cika Umrarsa,Insha Allahu.

BAYANIN YADDDA AKE AIKIN HAJJI.

AIKIN HAJJI:

akin Hajji De ya kasu kashi uku ne kamar yadda mukayi bayani adarasin baya Akwai:-

1.IFRADI.
2.QIRANI.
3.TAMATTU’I.

Sai mutum ya zabi wanda zai yi daga cikinsu, ga yadda Bayaninsu yake:-

1.IFRADI:- (Hajji kawai )
Wato yin niyyar aikin Hajji kadai kafin umara sai bayan ka gama aikin hajji anaso kayi aikin umara bayan ka gama kuma babu yankan hadaya akan ka.

2. QIRANI:-(wato gwamawa ko ace Hadawa)

wato hada aikin hajji da umara lokaci guda, batare da raba tsakanin su datareda kwance harami ba. Shikuma Zakayi hadaya bayan ka gama aiki.

3. TAMATTU’I (Jin Dadi)

Tamattu’I wato aikin Hajji na jindadi shine kayi aikin umara cikin watannin aikin hajji sannan ka cire harami,
kuma kayi duk abinda ya haramta ga wanda yayi harama yayi sannan ranar takwas ga watan zulhijja ranar tarwiyya a masaukin ka sai kayi niyyar aikin hajji. Amma in kagama aikin sai ka yanka hadaya.

To Abu nagaba kuma se ranar Tarwiyya wato takwas (8) ga watan Zul-hijjah, mai Qirani da mai Ifradi sai su tafi Mina haka nan ma mai Tamattu’i a wannan rana ne zai mayar da ihraminsa kuma ya yi harama daga inda yake ya nufi Mina Da safe daidai lokacin Walaha, kafin rana karkata ta bar tsakiyar sama, A Mina zasu yi sallar Azahar da La’asar (Kasaru, wato raka’a biyu-biyu), Magariba yadda take, Ishah (Kasaru, wato raka’a biyu), har su kwana ayi sallar Asubah yadda take ita ma.
Kowacce sallah za’a yi ta a lokacinta. Ana so mai harama ya yawaita yin Talbiyya da Addu’o’i. har gari ya waye wato ranar Arfa 9 ga Zul-hijja).
Daga nan sai tafiya Filin Arfa (ran (9)ga Zul-hijja).

RANAR ARFA

(9)ga watan Zulhijja, Bayan hudowar rana, sai masu harama gaba daya su baro filin Mina zuwa filin Arfa suna masu daukaka sauti da yin Talbiyya.
Bayan Annabi (SAW) ya baro filin Mina, ya tsaya wurare biyu Namra da Urna, to amma a yanzu mafi yawan masu harama ba sa samun ya da zango a wadannan wurare saboda cunkoson jama’a. Don haka ga duk wanda bai samu damar tsayawa ba ya iya wucewa zuwa Arfa. A nan ne liman zai yiwa masu harama huduba kuma a yi sallar Azahar da La’asar da kiran sallah daya, da ikama biyu kuma ba a nafila a tsakaninsu, Kuma Kasaru, wato raka’a biyu-biyu a madadin hudu-hudu.

Tsayuwar nan tana kasancewa tun daga hudowar rana har zuwa faduwar rana. Babu laifi a kowane hali mai harama ya sami kansa, ko a tsaye ko zaune ko a kishingide ko a kwance ko a tafe ko a haye ko a barci ko a ido biyu duk aikinsa ya inganta.
Kai ko da ma wani sashi na wuni ko dare ya tsaya a Arfa, to Hajjinsa ta inganta a wajen jumhurin Malamai.

Ana so mai tsayuwar Arfa ya yawaita addu’a saboda Hadisin da Annabi (SAW) yake cewa: Mafificiyar addu’a ita ce: addu’a ranar Arfa, kuma mafificin abin da na fada ni da duk Annabawa da suka gabace ni shi ne:

(لاَ إِلَـهَ إِلاَّ اللهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ)

LA ILAAHA ILLALLAHU WAHADAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WAHUWA ALA KULLI SHAI’IN KADIR.

Alhazai za su zauna a filin Arfa har sai rana ta fadi, bai halatta mutum ya bar filin Arfa kafin faduwar rana ba, in kuma an bari kafin faduwar rana to sai an yanka dabba (Fidiya).

Daganan se

ZUWA MUZDALIFA

Bayan rana ta fadi, sai kuma a tafi Muzdalifa cikin nutsuwa a can ne za a sallaci Magariba da Isha da kiran sallah daya (Ita Ishar Kasaru, wato Raka’a biyu). A nan ma za a ci gaba da yin Talbiyya. A nan dukkan masu harama za su kwana har su yi sallar Asuba. Sannan sai a tafi zuwa Mash’arul Haram (Mash’arul Haram dai wani karamin dutse ne a kusa da Muzdalifa) a nan za a tsaya a yi zikiri da addu’a.

Sai kuma

KOMOWA MINA DON JIFA

A ranar goma (10) ga Zulhijja wato yaumun nahar (ranar babbar sallah), masu harama zasu tafi tun kafin hudowar rana cikin nutsuwa zuwa Mina domin jifan jamrorin nan guda uku suna masu Talbiyya.
An so idan sun zo wani wuri da ake kira Badnul Muhassir su yi sauri kadan.
An so a tsinci Stakuwan jifan a Mina ba a Muzdalifa ba. A rana ta farko (Wato ranar Sallah Babba) zakajefi babbar Jamra ne kawai wato Jamratul Akaba sau bakwai ga kowacce daya idan ka jefa sai kayi kabbara. Shi wannan jifa wajibi ne a bisa zance mafi rinjaye.
To, daga wannan jifa ne aka halattawa mai harama yin duk abubuwan da aka hana shi saboda ihrami, in ban da saduwa da mata.

Har a wannan lokaci ba zai kusanci mace ba.
Daga nan sai soke ko yanka abin hadaya a wannan rana.
Kuma wajen sukar a Mina ne, to amma ya halatta a yi a ko’ina cikin Makka. Wanda bashi da kudin yin hadaya sai yayi azumi guda goma(10) azumin uku zeyi a Hajji, bakwai kuma idan ya dawo garinsu.
Sannan sai yin aski.

To amma yin aski ga maza ne kawai su kuma mata sai su aske gwargwadon tsawon gabar dan yatsa. Kamar yadda ya tabbata a hadisin Abu-Dawud.
Daga nan sai koma Makkah yin Dawaful Ifadha.

DAWAFUL IFADHA

Annabi (SAW) ya yi wannan dawafi a ranar Suka (Yaumun Nahar), amma ya halatta a jinkirta shi har zuwa karshen wata. Kuma sifar Dawafin nan ita ce dai irin yadda ta gabata abaya (Dahwaful Quudum)
sai dai ba zai yaye kafada ba kuma ba zai yi sassarfa ba. Bayan ya yi Dawafin sau bakwai sai kuma ya yi nafila a Makamu Ibrahim. Sai kuma ya je ya sha ruwan zam-zam.

Wanda yake Hajjin Tamattu’i sai ya wuce ya je ya yi sa’ayi a tsakanin Safa da Marwa.
Amma mai Qirani ko Ifradi ba lallai ne sai ya yi wannan sa’ayi ba, sai dai idan dama bai yi ba.
To daga nan ne aka halattawa mai harama aikata duk abin da a da aka hana shi hatta kusantar iyali domin aiki yazo Qarshe ,
Sai kuma a sake koma Mina a kwana a Mina, a kwanakin yanyane (Ayyamut-tashriq) wato tun daga 11 har zuwa sha uku ga watan Zulhijja.

A wannan kwanaki uku, kullum mutum zai je ya jefi jamrorin nan guda uku da tsakwankwani bakwai. Idan ya jefi ta farko (kanana). Sai ya tsaya ya fuskanci Alkibla ya yi addu’a.
Sai kuma ya jefi ta biyu, sai ya kuma fuskantar Alkibla ya yi addu’a.

Sai kuma ya jefi ta karshe (Babba), amma daga nan zai wuce ne ya tafi ba tare da ya tsaya ya yi addu’a ba.
Daga jifa na ranar sha uku (13) sai kuma dawaful Wada’i:
shi ne dawafin bankwana. Ga wanda zai fita daga Makka don komawa garinsu sai ya je ya yi dawafi kamar dai yadda aka siffanta a baya.
Sai dai shi wannan dawafi babu sharadin sanya Ihrami a jikinsa mutum zai iya yi da kayansa na al’ada. An yi wa mace mai haila rangwamen yinsa matukar dai ta yi Dawaful Ifadha.

Wannan shi ne yadda ake aikin Hajji a Aikace.

Dafatan Allah yakaimu Hajji musauke farali lafiya.

Ameen.

08031106304.

Ads