Share this on:
 • 50
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  50
  Shares

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta ce ba za ta fito a fim din da ya ci karo da addininta na Musulinci da kuma al’adunta ba. Ta bayyana haka ne sakamakon soma fitowa da ta yi a fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.

“Fitaccen jarumin Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani fim dinsa mai suna ‘Lagos real fake life’.inji gabon

takuma kara dacewa “Shi ne furodusan fim din kuma na fito ne a matsayin ‘yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta bahaushiya don haka kayan da nake sa wa a fina-finan Kannywood
irinsu nake sa wa a wannan fim din”

“Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a fim dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Ba zan fito a matsayin da zai saba da addini da al’adata ba”

A cewarta, “Ba wannan ne karon farko da na soma yin fim da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a wani gajeren fim na turanci, amma wannan ne karon farko da na fito a fina-finan Nollywood.

Hadiza Gabon ta kara da cewa babu wani “bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finan Kannywood da na Nollywood idan ban da bamabancin harshe. Don haka na ji dadin soma fitowa a fina- finan Nollywood”.


Share this on:
 • 50
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  50
  Shares