Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Fitacce kuma babban jarumi a masana’antar kannywood Ali Nuhu ya kaddamar da bikin bude katafaren shagon siyar da kayayyaki jiya a birnin kanon dabo.

A cikin shagon wanda aka bude a nation plaza shago mai lamba 10 dake kan titin Audu Bako cikin birnin Kano, wanda jarumin ya yiwa lakabi da Don Ali Collections, za’a rika siyar da kayayyakin sanyawa a jiki kama daga takalma zuwa riguna, jerseys, underwear da dai sauransu.

Kaddamar da bude shagon ya samu halartar mutane da dama daga ciki da wajen birnin Kano. Daga cikin mahalartar bikin bude shagon akwai manyan yan kwallon kafar nan guda biyu, wato Ahmad Musa, Da abokin sa Shehu Sokoto.

A bangaren yan film da suka halarci bude shagon akwai Sani Danja, Yakubu Muhammad, Abdul amart, Ramadan booth, Aminu S Bono, Abubakar mai shadda, Misbahu anfara da dai sauransu.


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •