Labarin da muke samu da dumi-dumin sa yanzu na nuni da cewa masana’antar Kannywood na shirin kamawa da wutar rikici babba bayan da alamu ke nuna cewa babban rikici ya barke a tsakanin jarumar nan da aka kora Rahma Sadau da kuma uban gidan ta watau Ali Nuhu.

Rahama Sadau Ta Shiga Cikin Jerin Mata Uku Masu Tashe A Arewa

Wannan rikicin dai ya far fitowa fili ne sakamakon yadda wasu manya jigogi kuma makusantan jarumi Ali Nuhu din suka fito a kafafen sada zumunta na manhajar Instagram suna aibata jaruma Rahma Sadau da munana kalamai da kuma zagi.

Dan karamin binciken da akayi an gano cewa musabbabin rikicin bai rasa nasaba da rashin goron gayyata da Ali Nuhu bai ba Rahma Sadau din ba wajen shirya wani sabon film din sa Abota da ita kuma take ganin kamar ba’a yi mata dai dai ba. Abubuwa Biyar 5 Da Sukafi Tayar Da Hankali A Masana’antar Film Din Hausa Kannywood

Shi dai Ali Nuhu tamkar wani bango ne a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood inda yake matsayin yaya ko kuma ma uba ga da yawa daga cikin
jaruman fim din musamman ma mata.

Haka ma dai mun samu cewa Ali Nuhu din shine musabbanin shigowa da Rahma Sadau harkar fim kuma shine dalilin shaharar ta saboda sanya ta da
yayi a cikin wasu fina-finan sa.

To kome zakuce?????

daga naij hausa

Ads