Share this on:
 • 28
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  28
  Shares

Da zafi-zafi! MTN Na Bayar Da Kyautar 1GB Akan N200 Kacal

Jama’a barkanku da kasancewa damu a arewamobile a wannan lokaci na yammacin ranar laraba.

Wannan wani sabon tsari ne na data da kamfanin MTN suka bullo da shi inda suke bawa masu amfani da layukan su data ta browsing akan kudi kalilan.

Shidai wannan tsari sunyi masa lakabi da “welcome back offer” wanda tsari ne da yake baiwa mutum damar more garabasar data da takai 1GB akan Naira 200 kacal. Kuma tana yin aiki ne har na tsawon kwana bakwai.

Sai dai ba kowanne layi bane zai iya more wannan garabasa, mafi yawancin layukan da za’a iya samun wannan garabasa akansu sai layukan da aka dan dauki lokaci ba’ayi amfani da su ba.

Domin dubawa ka gani ko ka cancanci more wannan garabasar ko akasin haka sai ka danna *559*65# inda zasu turo maka sakon cewa zaka iya morewa ko kuma a’a.

Bayan danna wadancan lambobi dake sama, in ya kasance kana jerin wadanda zasu iya more wannan garabasa sai kawai ka sanya katin MTN na N200 sai ka dannan wadannan lambobi *131*65# sannan sai ka kira. Shikenan zasu kwashe N200 da ka sanya sai su baka 1GB wacce zaka yi har tsawon sati daya kana amfani da ita.

Tura ma abokanka…


Share this on:
 • 28
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  28
  Shares