A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 16 zaku ga irin wainar da ake toyawa a gidan kamaye inda matar shi Adama keta faman gasa mashi aya a hannu dangane da harkar abinda ya shafi tarbiyar ya yanshi gami da batun ilmin su.

dadin kowa episode 16

Dangantaka tsakanin Sallau da Dantani sai kara tsami take inda ya kasance kullum sai anji kansu suna hayaniya, wanda har sai da ta kaiga an shiga tsakaninsu.

Gimbiya dai nata kara fuskantar tsanani a gidan da take aikatau saboda Bintu ta kara tasa ta a gaba bisa kishin cewa akwai alamar alaqa ta soyayya tsakaninta da IB.

Wadannan dama sauran wasu batutuwan na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 16

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 16

Ads