A satin daya gabata cikin shirin dadin kowa sabon salo kun ga yadda halin kunci a gidan malam ayuba ke kara tsananta ta fannin ciyarwa da kuma karin abubuwan da suka shafi rayuwa.

Sannan kunga dawowar sallau garin dadin kowa a firgice wanda hakan yasa ake mashi kallon mahaukaci da sauransu.

A cikin wannan satin zaku ga yadda gimbiya ta dage wajen ganin sun sami saukin rayuwar da suke ciki.

Malam Ayuba dai kullum abu sai kara cigaba yake, babu wani dadi a zaman gidansa.

Garbati yaron malam ya fara gane lunguna da saquna na cikin garin dadin kowa, zaku ga abinda zaiyi.

Kamaye kuma yan awon fili abubuwa sun dau zafi, zaku ga yadda ta kaya.

Shin wane hali Chioma da mijinta Ojukwu suke ciki a halin yanzu? Ku kalli wannan shiri na dadin kowa sabon salo episode 2 a zangon youtube na tashar Arewa24.