A cikin wannan sabon shirin na dadin kowa sabon salo episode 10 zaku ga yadda danganta ke kara tsami tsakanin Bintu da Gimbiya saboda tunanin Bintu na ganin kamar Ib yana son Gimbiyar.

Zaku ga yadda harka ta kara kankama tsakanin Goga da Harisu almajirin malam na ta’ala biyo bayan damar da ya samu daga malam na ta’ala akan su cigaba da hulda tare.

A bangare guda kuma alamu na nuni da cewar cikin Hafsatu yayi kwari don har ta kaiga ta fara zuwa ganin likita, wanda da zarar ta haihu lafiya zata bar gidan malam Musa tunda dama babu igiyar aure a tsakanin su.

Da sauran abubuwan da zaku gani a cikin wannan shiri na dadin kowa sabon salo kashi na goma..

Ads