A cikin wannan sabon shirin na dadin kowa sabon salo kashi na 14 zaku ga yadda alaqa tsakanin dan tani da sallau ke kara tsami.

Halin kunci kullum sai kara dabaibaye kamaye yake, kama daga matsalar rashin kudi zuwa kuma matsalar rashin fada aji ko kuma rashin karfin iko a gidan shi.

Delu cogal dai kuma abu ya kara cabewa biyo bayan ziyarar ta zuwa kauyen su malam kabiru makaho wanda a can ta fahimci cewa da alamu dai malam Kabiru makaho dai yayi mata karya…

Wadannan dama sauran batutuwan na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 14

Ads