Share this on:
 • 2
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  2
  Shares

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 18 Arewa24

A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 18 zaku ga yadda al’amurra suka nemi su cabe wa Sabuwa matar malam Ayuba biyo bayan kwankwasa kofa da Isa me kanti yayi mata don ya karbi kudin bashin da yake binta.

Adama kuma hankali ya dugunzuma domin ko yau kwana biyu kenan ba’a ga mijinta ba wato Kamaye awon igiya tun bayan yar hayaniyar da ta auku tsakaninsu, shin ko Kamaye na nan a raye?

Da alamu dai Dantani mai shayi ya fara kamuwa da son Halimatu wato tsohuwar matar malam Ayuba kenan duk da dai shima Audi wato aminin malam Ayuba shima ya bayyana tashi maitar a fili.

Zaku ga yadda malam Ayuba ya gamu da gamonsa a wajen bibiyar mata da yake yi.

Sai ku kalli wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 18 a tashar youtube ta Arewa24 dake kasa

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 18 Arewa24


Share this on:
 • 2
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  2
  Shares