A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 19 zaku ga yadda iyalan Kamaye ke cigaba da zama a cikin jimami na rashin sanin inda yake na wasu yan kwanaki.

Zaku ga yadda hafsatu keta faman kara caja wa malam Musa kayi domin idan yasa mata doka bata bi sai dai ta sa kafa tayi fatali da ita, amma fa daga karshe malam Musa ya dauki mataki.

Daga karshe dai Adama ta gano inda mijinta wato Kamaye ya boye to amma sai dai yaki yadda ya koma gida inda daga karshe har yayi ikrarin tsundumawa cikin duniya.

IB dai ya bayyana wa Gimbiya yar gudun hijira abinda ke cikin zuciyar shi. Sai dai kuma ko ya zata kaya biyo bayan yunkurin da Yana take na ganin anyi Ibrahim din baiko da Bintu….

Ku kalli wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 19 daga tashar youtube dake kasa…

Ads