Share this on:
 • 22
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  22
  Shares

A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 20 zaku ga cewa hankalin Hafsatu ya tashi sosai a dalilin yunkurin malam Musa na tursasa ta akan zuwa asibiti don tabbatar da cewa ko cikin nan nata na nan koko ya zube.

Da alamu dai Alhaji mai gidan haya ya fara kyasawa akan yar uwar Gimbiya wato Sa’adatu inda da alamu yayi mata tayin aure.

Ibrahim IB nata kokarin ganin cewa Gimbiya ta bashi amsar bukatar shi da ya furta ta soyayyarsa a gareta, amma da alamu dai tana jin tsoron bashi amsa. Sai dai kuma abinda shi bai sani ba ashe tuni Yana ta riga da ta gama tsara mashi komai na batun a hada shi aure da Bintu.

Malam Ayuba dai ya je ya karo sabon shiri don tunkurar Tani wanda da alamu ya fara samun shiga. Sai dai kuma bai damu da halin da danshi dan Asabe ke ciki ba wanda yake a gida kwance ba lafiya.

Shin ko Ib zai karbi shirin hada shi da ake yunkurin yi da Bintu baya ga kuma ya riga da ya furta kalmar so ga Gimbiya.

Ku kalli wanna sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 20 daga tashar youtube ta Arewa24 dake kasa

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 20 Arewa24


Share this on:
 • 22
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  22
  Shares