A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 22 zaku ga yadda take kaya wa a gidan malam Musa tsohon soja wanda ya kasa fahimtar cewa babu wani ciki da Hafsatu ke dauke da shi illa iyaka dai kawai tana yaudarar shi ne.

Shi kuma Kamaye abubuwa sai kara tabarbarewa suke a gidansa domin kuwa matar shi Adama ta hana shi sakat musamman wajen ganin ya baiwa yaranshi tarbiya me kyau.

Malam Tsalha ya kunno wa su Gimbiya wuta daga wajen mai gari inda har ta kaiga Alhaji Buba yanke shawarar tunkarar Gimbiya da maganar aure. Ko yaya zasu kaya?

Goga na kokarin koya ma yaronsa wato Harisu shaye-shayen miyagun kwayoyi wanda har ta kaiga ya fara busa mashi hayakin wiwi wanda hakan ya jawo wa malam Nata’ala tunanin cewa ko Harisun yayi gamo ne.

Kyauta dillaliya dai ta dage sosai wajen ganin cewa ta saka Sa’adatu wato yar uwar Gimbiya cikin harkar safarar yan mata da ake yi, inda da alamu dai zata yi nasara sakamakon kasan fahimtar hakan da Sa’adatun tayi…

Wadannan dama wasu sauran abubuwa na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 22 daga tashar youtube ta Arewa24 dake kasa…

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 22 Arewa24