A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 23 zaku ga yadda take kara tsami tsakanin Gimbiya da yar uwar ta Sa’adatu dangane da aikin da Kyauta dillaliya take yunkurin samar mata.

Madam Gloria tana yunkurin korar Chioma biyo bayan kasawarta wajen kawo yan matan da za’a tura kasar waje don yin business.

Akwai yiwuwar Stephanie ta gane irin sana’ar da mahaifiyarta take wacce ta dade tana boye mata don kasantuwar sana’ar bata arziki bace.

Ko Ib zai hakura ya kyale Gimbiya kuwa?

Wadannan dama sauran abubuwa na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 23

Ku kalli wannan sabon shiri daga tashar youtube ta Arewa24 dake kasa

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 23 Arewa24

Ads