Dadin Kowa Sabon Salo Episode 24 Arewa24

A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 24 zaku ga yadda take kara tsami a gidan malam Musa inda Hassatu ke kokarin ganin ta kuntata ma Baraka ta hanyar izgili da take mata akan mijinta.

Gimbiya na kara fuskantar tsangwama daga gurin Bintu duk da dai alamu na nuni da cewar Ib ya hakura da ita Gimbiyar tunda har ya fara karkatowa wajen Bintu.

Shirye-shirye sai kara kankama suke akan tafiyar yar uwar Gimbiya wato Sa’adatu zuwa kasar waje domin domin yin aikin da Kyauta dillaliya tayi mata hanya ta hannun madam Gloria, ko yaya zata kaya?

Malam Audi dai sai kara matsawa yake don ganin an gaggauta daura mishi aure da Halima, wato tshohuwar matar malam Ayuba da ya saka.

Wadannan dama sauran abubuwa na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 24.

Ku Kalli wannan sabon shiri daga tashar youtube ta Arewa24 dake kasa

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 24

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 25 Arewa24

A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 25 zaku ga yanda malam Musa da baraka ke gumawa Hansatu haushi wanda har hakan yayi sanadiyyar ta kai karar shi wajen dan uwanta Audi.

Sa’adatu dai ta nace akan batun tafiyar ta zuwa aikatau kasar waje duk da kokarin da Gimbiya take na ganin ta hana ta wanda hakan ke kokarin gagara domin kuwa har ta kaiga ta tafin yin passport don ayi mata Visa.

Malam Ayuba yaki biyan jama’a basussukansu dukda cewar anyi albashi. Hatta a gidan shi ma aabai nuna alamun samun kudin da yawa ba. Ko ya zata kaya tsakanin shi da malam Audi.

Zaku ga yadda zata kaya tsakanin Goga da ogansa wato oga Charlie

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 25

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 26 Arewa24

A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 26 zaku ga yadda harka take nema ta kullewa goga biyo bayan dena kawo masa kaya da Ogansa Charlie yayi.

Madam Gloria ta budo wuta akan yunkurin tafiyar Sa’adatu zuwa kasar waje, wanda har ta kaiga suna shirin tafiya Lagos, ko yaya zata kaya?

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 26

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 27 Arewa24

A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 27 zaku ga yadda jikin Gimbiya ya tsananta sosai wanda har hakan ya dakatar da tafiyar yar’uwarta zuwa Lagos don tafiya kasar waje.

Da alamu dai Mudi ya gaza cika aikin da malaminsa ya sanya shi wanda har haka ta jawo za’a canza mashi gurin zama, ko wanne irin aiki ne Mudin keyi?

Ibrahim IB ya yanke shawarar zuwa asibiti don ya gaishe da Gimbiya sannan kuma ya duba yanayin da take ciki.

Aunty Yana ta fara korafi akan rashin zuwan Gimbiya wajen aiki a inda tayi ikrarin korarta gami da dauko wata yar aikin.

Madam Gloria ta bukaci da Sa’adatu ta mayar mata da duka kudaden da ta kashe akanta tun lokacin da aka fara maganar tafiyarta zuwa kasar waje, ko menene yayi zafi?.

Zaku ga dawowar alawiyya a cikin wannan sabon shiri..

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 27