A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 28 zaku ga yanda Alawiyya ke jimamin gidan su na da a garin dadin kowa, sannan kuma kuji ko wane dalili ne ya kawota garin dadin kowa.

Jikin Gimbiya dai sai kara tsananta yake inda daga karshe har ya kasance bata iya zuwa gidan aikinta, wanda hakan ya jawo Yana ta fara tunanin korarta daga aikin nata.

Zaku ga yanda ta kaya tsakanin Sa’adatu da mutanen gidan aikin Gimbiya wato Aunty Yana da kuma diyarta Bintu.

Zaku ga sababbin fuskoki a cikin wannan sabon shiri na 28; kamar su Alawiyya, Wizzy, Kaka, da Kuma Zayyad.

Daga karshe zaku ga cewa bomb ya kara fashewa a sabuwar police station ta dadin kowa a yayin da Alawiyya da Wizzy suka je don jin labarin Dan uwanta Aminu, shin ko hada su harin bomb din ya rutsa?

Wadannan dama sauran abubuwa na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 28

Ku sauke shi daga tashar youtube ta Arewa24 dake kasa

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 28 Arewa24