A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 29 zaku ga cewa hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta fara bincike akan sabon harin bomb da yan ta’adda suka kai a police station din dadin kowa.

Alawiyya ta samu raunuka a jikinta a yayin aukuwar ibtila’in tashin bomb din a yayin da akalla mutum uku suka rasa rayukansu wasu kuma suka jikkata.

Zaku ga yadda Dan asabe wato dan wajen malam Ayuba ya buge da shaye-shaye sakamakon halin matsi da kuncin rayuwa da ya tsinci kanshi a yayinda mahaifinsa malam Ayuba ke yunkurin ganin ya auri Tani.

Alawiyya dai ta matsa kaimi wajen ganin cewa ta samu labarin inda za’a iya ganin dan uwanta Aminu A. K wanda hakan shine sanadin barowar ta kauyensu zuwa garin dadin kowa, ko bukatar tata zata samu biyuwa.?

Hukumar jami’an farin kaya tana kara matsa kaimi wajen ganin ta binciko yan ta’addan dake kokarin kara jefa garin dadin kowa cikin rudani ta hanyar ayyukan ta’addancin su.

Zaku ga yadda ta kaya tsakanin Tani da malam Ayuba a yayin da yake kara matsa mata lamba akan maganar aurensu.

Wadannan dama sauran abubuwa na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 29.

Kalle shi a tashar youtube dake kasa

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 29