A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 30 zaku ga cewa malam Ayuba ya kwashi zubin farko na adashin malanan makaranta da malam Nura ke yi biyo bayan sa hannu da yayi, inda aka bashi zabar kudi har naira dubu dari biyu..

Tura fa tana nema ta kai bango, domin ko matar malam Ayuba wato sabuwa ta fara gajiya da wannan ukuba da take sha a gidan malam Ayuba, sakamakon hakan take ganin a shirye take da ta karbi ko wanne irin mataki zai dauka.

Kurunkus! Malam Musa ya jajirce akan lallai sai Hafsatu taje asibiti an yi mata gwajin ciki don tabbatar da cewar ko akwai cikin nan ko kuma babu. Ko yaya zata kaya?

Wadannan dama sauran abubuwa na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 30.

Ku kalle shi daga tashar youtube dake kasa

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 30

Ads