Share this on:
 • 19
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  19
  Shares

A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 31 zaku ga yadda bala’i da masifar dake faruwa tsakanin Hafsatu da malam Musa ta rikede ta dauki sabon salo.

Goga ya fita farautar wanda ya daukar masa kudinsa dukda dai yafi zargin Gaye, sai da ya nemi ya cima Dan Bayero mutunci, amma daga bisani ya karbi kudin sa a hannun Gaye.

Delu cogal ta sake bayyana a gidan su Gimbiya biyo bayan labarin da ta samu na cewar Alawiyya tazo garin dadin kowa.

Zaku ga sabuwar rayuwar da hukumomi ke kokarin sanya Aminu A. K da abokin sa Rambo a yayin da suke zaune a wajen jami’an tsaro, ko kwalliya zata biya kudin sabulu, sannan kuma ko zasu yi nadamar rayuwar su ta baya?

Malam Bala ya shiga tsakanin Hafsatu da malam Musa don sansanta rigimar dake tsakaninsu inda ya basu shawarar abinda ya kamata suyi don tabbatar da samun zaman lafiya a gidan nasu.

Alhaji Buba ya bi shawarar da Alhaji Mala ya bashi akan ta yadda zai bullo ma Gimbiya, shin ko hakarshi zata cimma ruwa?

Wadannan dama sauran abubuwa na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 31.

Ku kalle shi a tashar youtube dake kasa

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 31


Share this on:
 • 19
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  19
  Shares