A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 32 zaku yadda Bintu da Sa’adatu yar uwar Gimbiya ke cigaba da zaman doya da manja inda har Sa’adatu tayi yunkurin lakadawa Bintu duka.

Alaka tsakanin Stephanie yar Madam Gloria da Nasir dan wajen Malam Hassan na neman dawowa tayi karfi fiye da da, ko Gloria zata bar hakan ta faru.?

Da alamu dai Dantani mai shayi ya karbi shawarar da Dan Bayero ya bashi akan ya nemi auren Halimatu, ko wannan batu zai yima malam Audi dadi duba da cewar shima yana neman Halimatu?

Zaku ga yadda malam Hassan ke kokarin ganin ya inganta rayuwar dalibansa ta yadda yake kokarin nema musu guraren da zasu koyi sana’o’i don dogaro da kansu da kuma kokarin sama musu hanyar da zasu sami ilmin zamani don zamantakewa.

Wadannan dama sauran batutuwa na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 32.

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 32 Arewa24

Ads