Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 34 zaku ga dawowar badaru dan dan Malam Musa tsohon soja gida a yayin da suke tsaka da zaman doya da manja da Hafsatu.

Zaku ga yadda al’amurra ke gudana a gidan malam Ayuba mai gadi na wulakanci da karin halin ko in kula da uwar gidan shi ke kara fuskanta daga gareshi. Ko menene ke kara janyi hakan?

Shin kowace waina Hafsatu da kawarta Kyauta dillaliya ke toyawa don ganin sun sami damar cigaba da abinda suke so a gidan malam Musa?

Ko wane hali Dan asabe zai shiga sakamakon halin matsi da kuncin rayuwa da ke damunsa inda har aiki ya nemi a bashi a shagon dinki amma abin ya ci tura?

Sai ku kalli wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 34 a tashar youtube dake kasa..

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 34


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •