Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

A satin daya gabata cikin shirin dadin kowa sabon salo kun ga yadda
sallau ya kwace daga asibiti ya shigo gari don ganin yazo ya dau mataki akan dantani da ya ke ma kallon maci amana.

A cikin wannan satin zaku ga yadda madam Gloria ke ta kokarin fara safarar yan mata zuwa kasar waje.

Su dantani sun kawo sallau wajen malam Hassan don ayi masa ruqya.

Rayuwa sai kara tsanani take wa su gimbiya da yar uwarta sa’adatu inda a har ta kaiga an basu notice din cewa su tashi daga gidan da suke.

A bangare guda kuma, malam ayuba na ta yunkurin kara aure duk da cewar ba ya iya fita hakkin iyalanshi wanda har hakan ya kaiga an kira shi zuwa gidan mai gari, inda daga bisani ya karbi yayan shi daga gurin tsohuwar matar shi sannan kuma ya yanke shawarar tura su makarantar allo..

Ku sha kallo daga channel din youtube na tashar Arewa24 dake nan kasa..


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •