Share this on:
 • 7
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  7
  Shares

A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 44 zaku ga yadda su Alawiyya ke kara shiga cikin damuwa da tsangwama daga wajen matar mahaifinsu wato Delu cogal wacce take kokarin ganin cewa ko kadan bata barsu su Numfasa ba.

Malam Musa na shirin mayar da Hafsatu dakinta wanda hakan ke neman ya janyo matsalar daka iya kawo karshen zaman shi da matar shi Baraka. Shin ko maganin da Hafsatu ta zuba masa a abinci ne ke aiki?

Malam Habu da malam Bello mahaifin Nazeer sun zo gidan malam Kabiru Makaho don su nema wa Naziru iznin neman auren Alawiyya, shin ko haka zata cimma ruwa duba da cewa shi malam Kabiru yana son ya kasance Alhaji Buba ta aura?

Baraka dai takaici ya ishe ta, wanda sanadin hakan ne ma yasa tayi yaji da zummar cewa baza ta kara dawo wa ba muddun Hafsatu bata bar gidan ba, sai dai kuma Dr. Amina ta bata wata shawara. Shin ko shawarar mai bullewa ce?

Zaku ga yadda malam Kabiru Makaho suka yi kaca-kaca da Alhaji Buba biyo bayan maganar da malam Kabirun yayi masa ns cewar ya auri yar sa Alawiyya ya kyale Gimbiya.

Sanarwa ta musamman daga tashar Arewa24 : A bisa wasu yan sauye-sauye da tashar tayi, shirin dadin kowa sabon salo da ake dorawa a YouTube channel a yanzu zai rika zuwa muku ne ranar Asabar da misalin karfe 9 na dare, wato bayan an gama kallon shi a akwatin talabijin daga karfe 8 zuwa 9

Ku kalli wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 44 a tashar youtube da ke kasa


Share this on:
 • 7
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  7
  Shares