Share this on:
 • 66
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  66
  Shares

A cikin wannan shiri na dadin kowa sabon salo episode 79 wanda ke zuwa muku daga tashar talabijin ta Arewa24 zaku ga yadda masu karbar wutar lantarki ke karbar na goro a hannun jama’a don su daga musu kafa wajen yanke wutar. Ko yaya zasu kare idan asirin su ya tonu?

Da alamu dai Alhaji Buba na neman ya shiga tsaka mai wuya, biyo bayan batan dabon da motar Alhaji Mala ya bashi ajiya a matsayin jingine tayi a cikin gidansa. Waye ya dauke ta kuma Ko yaya zata kaya?

Karatun Bintalo dai yana ta kara fuskantar kalubale iri-iri inda har ta kai ga an koro ta daga makaranta kan rashin siyan wasu litattafai wanda Aminu Ak keta kokarin ganin an samun kudin litattafan don ta koma makaranta ta cigaba da Karatu. Ko haka zata cimma ruwa?

Shin Ibrahim IB ya fara son Bintu ne a zuciyarsa Duba da Yadda ya fara nuna halin kulawa a gareta musamman a halin da take na rashin lafiya wanda har ya kaiga dafa mata abinci ci?

Zaku ga yadda tsohuwar budurwar Nazir wato maryam ke yunkurin ganin ta kashe ma Nazir din aurensa inda har tayi yunkurin karbar lambar sa a gurin IB, ko hakar tata zata cimma ruwa kuwa?

Wadannan dama sauran wasu batutuwan na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 79. Zaku iya kallon wannan shiri ta tashar youtube din gidan talabijin na Arewa24 dake kasa..


Share this on:
 • 66
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  66
  Shares