Share this on:
 • 92
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  92
  Shares

Stephanie

Stephanie dadin kowa

A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 80 zaku ga yadda Samuel ke ta faman ganin ya shawo kan Stephanie akan juyo da akalar soyayyar ta zuwa gare shi. Zaku gani ko zai yi nasara ko akasin haka.

Da alamu dai kyauta dillaliya ta gaji da rikon Madu, dan-dan Gimbiya yar gudun hijra inda har ta fara yunkurin daukar shi ta kaima Madam Gloria ta rike shi don itama taji abinda ake ji.

Shin ina aka kwana ne kan batun Dan baba, yaron Alhaji Buba da ya ture Malam Kabiru Makaho da motar Alhaji Mala da suka dauko a garejin gidansu?

Tsaka mai wuya: Stephanie da iyayenta na cikin rudani saboda kin amincewa da tayi da soyayyar Samuel wanda hakan ke neman yin barazana ga jin dadi da walwalarsu

Wadannan dama sauran wasu batutuwan na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo episode 80. Domin kallon shi sai ku shiga YouTube channel na tashar Arewa24 dake kasa

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 80


Share this on:
 • 92
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  92
  Shares