Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

A cikin wannan shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 81 za ku ga yadda Malam Kabiru Makaho tare da matarsa Delu cogal wato macogala ke yunkurin hana Bintalo cigaba da zuwa makaranta.

Jikin Bintu dai yayi tsauri sosai inda har ta kai za’a yi mata maganin kumburin hanji gami da kuma ciwon gyambon ciki wato olsa(ulcer) dake inda likitocin suka bukaci a biya zunzurutun kudi har naira dubu dari uku da hamsin(350k), a yayinda alhaji mala ke fama da karancin kudade a hannun shi, ko yaya zata kaya?

Malam Musa tsohon soja nata yunkurin ganin ya dawo da tsohuwar matar shi Hansatu, sai dai kuma yana fuskantar barazana daga matar shi da suke tare wato Baraka wacce ta kekashe kasa akan cewar ba zata zauna gida daya da Hansatu ba.

Ana kokarin kashe auren su Nazir da Alawiyya, ko su waye da kokarin aikata wannan danyan aikin kuma ko menene ribarsu akan hakan?

Wadannan dama wasu sauran batutuwan na nan a cikin shirin dadin kowa sabon salo kashi na 81.

Ku sauke wannan bidiyo daga tashar YouTube ta gidan talabijin din tashar Arewa24 dake kasa

Dadin kowa sabon salo episode 81


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •