Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

A cikin wannan shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 83 za ku ga yadda abokan aikin alhaji mala ke kokarin kunno masa wuta biyo bayan fahimtar da suka yi cewa alhaji Mala ya siyar da transformer. Shin ko hakar su zata cimma ruwa?

Da alamu asirin headmaster ya tonu domin kuwa an turo daga ma’aikatar ilmi akan azo ayi bincike bisa cuwa-cuwar da yake yi ta karbar kudi a hannun iyayen yara duk ko da cewa gwamnati ta dauke nauyin karatun ko wane yaro. Ko yaya zata kasance?

Take-taken Ibrahim IB na nuni da alamun cewa ya fara kamuwa da soyayyar Bintu sannan kuma har ya mance da Gimbiya inda ko sunanta ma bai so yaji an kira, shin adduar Bintu da ta mahaifiyarta taci kenan?

Hansatu dai ta samu damar tarewa a gidan malam Musa tsohon soja bisa sharadin cewa ba zata rika tayar da fitina a gidan kamar yadda tayi da can ba. Ko hakan mai dorewa ne?

Wadannan dama wasu sauran batutuwan na nan a cikin shirin dadin kowa sabon salo episode 83.

Domin kallo gami da sauke wannan shiri sai kubi link dake kasa zuwa tashar YouTube ta gidan talabijin din tashar Arewa24

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 83

https://youtube.com/watch?v=X93BnFGdPOY


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •