Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

A cikin wannan shiri na dadin kowa sabon salo episode 84 zaku ga yadda take kayawa tsakanin Hafsatu da Baraka kan sace mata waya da akayi inda ita Baraka ke zargin Hafsatu da hakan. Shin ko yaya zata kasance.

Har yanzu Adama bata hakura ba wajen ganin ta zubar da cikin shegen diyarta wato Hannatu. Kyauta dillaliya ce dai ke kara zuga ta wajen aikata hakan duk da gargadi da mijinta wato Kamaye yayi mata na cewar karda ta kuskura ta kara yunkurin hakan.

Ashe dama an kori Malam Dan-Bala daga aikin koyarwar da yake yi a makarantar su Binta yar Malam Kabiru Makaho. Sai dai da alamu hakan baiyi masa dadi ba inda yayi ikrarin kawo ma takarar Ciyaman tarnaki, ko yaya zata kaya tsakanin su.

An fitar da sunayen wadanda suka samu takardar gurbin karatu a makarantar gaba da sakandire na bana. Dan-Asabe na cikin wadanda suka nemi wannan gurbi, inda har ya kashe zunzurutun kudi don ganin ya samu wannan dama, shin ko hakar Dan Asabe zata cimma ruwa?

Abokan aikin Alhaji Mala na yunkurin kunno masa wuta don ganin sun bashi matsala, sai dai ko zasu sami biyan bukatar su?

Wadannan dama wasu sauran batutuwan na nan a cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 84.

Domin kallon wannan shiri na dadin kowa sabon salo episode 84 sai kubi link na tashar YouTube ta gidan talabijin din tashar Arewa24 dake kasa

Dadin kowa sabon salo episode 84 Arewa24


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •