Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

A cikin wannan shiri na dadin kowa sabon salo episode 85 zaku ga yadda zata kaya tsakanin Kofur(cpl) Audu da malam Ayuba mai gadi wajen neman soyayyar Bilkisu mai abinci dukda dai akwai yiwuwar malam Ayuba ya koma wani wajen, shin ko yaya zata kasance? Kuma ko waye zaiyi nasara wajen karbe soyayyar tata.

Yan tsurku da tsugudidi na ta kara yunkurin ganin cewa sunyi iya duk yadda zasu iya wajen ganin sun wargaza auren Alawiyya da Nazir ta hanyar hada shi fada da mahaifiyar shi don cimma wasu bukatunsu na kansu, ko hakar su zata cimma ruwa.

Da alamu dai zaune bata kare ma Dantani mai shayi ba, domin kuwa kawun shi wato kawu Manu ya addabeshi ta hanyar jawo mashi matsaloli daban-daban, kama daga kokarin durkusar dashi wajen sana’ar shi zuwa ga wasu sauran matsaloli ma rayuwa. Ko ta yaya Dantani zai magance wannan damuwa tashi?

Adama matar Kamaye da kuma Kyauta dillaliya sun dage sai sun ga cewa sun kwantar da dan dake cikin Hannatu don rufa ma kansu asiri har zuwa lokacin da suke tsammanin zata iya samun miji sai suyi masa rufa-rufa su aura mata shi, ko zaau yi nasara akan hakan?

Wadannan dama wasu sauran batutuwan na nan a cikin wannan shiri na dadin kowa sabon salo episode 85. Domin kallon wannan shiri sai ku shiga link na tashar YouTube ta gidan talabijin din tashar Arewa24 dake kasa

Dadin kowa sabon salo episode 85


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •