Share this on:
 • 11
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  11
  Shares

A cikin wannan shiri na dadin kowa sabon salo episode 86 zaku ga yadda soyayyar Ibrahim IB da Bintu ke kara karfafa wanda da alamun hakan in har ta dore zai yiwa Aunty Yana da Alhaji Mala dadi sosai, ganin cewa abinda suka dade suna Buri kenan.

Da alamu dai Malam Ayuba mai gadi da gaske yake wajen neman auren Hannatu yar wajen Kamaye awon igiya, sai dai ko hakan mai yiwuwa ne duba da cewar matar shi Sabuwa tana sane da cikin shegen da Hannatun take dauke dashi?

Malam Nata’ala ya hassala sosai bisa canzawa Dantalle makaranta da akayi inda har yayi ikrarin daukar mummunan mataki akan abokin shi Malam tanimu da kuma Malam Hassan. Ko wane irin mataki yake shirin dauka?

Yan ta’adda sunyi ma Aminu AK tayin yazo su cigaba da aiki tare, inda suka turo mishi makudan kudade don karkatar da hankalin shi, shin ko zai karbi wannan tayi nasu.

Wadannan dama wasu sauran batutuwan na nan a cikin shirin dadin kowa sabon salo kashi na 86. Ku Kalle shi a tashar YouTube ta gidan talabijin din tashar Arewa24 dake kasa

Dadin kowa sabon salo episode 86


Share this on:
 • 11
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  11
  Shares