Share this on:
 • 149
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  149
  Shares

A cikin wannan sabon shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 87 zaku ga cewar Aminu Ak ya amsa gayyatar Malam Zayyad domin su tattauna wani abu dashi Malam Zayyad din ke son Aminu AK yayi masa. Ko menene zasu tattauna kuma ko AK din zai amince.

Zakara mai neman suna, ka ci tsakuwa ka bada tsaba, zaku ga yadda Malam Ayuba mai gadi ke ta dawainiya da gidan Kamaye biyon bayan iftila’in da ya afka ma Kamayen, duk wannan wai don yaga Hannatu yana so a bashi ya aura, ko ya zata karke.

Danbaba dai kullum sai kara janyo ma alhaji Buba bala’i da masifu iri-iri yake, ta yau daban, ta gobe daban inda har yake neman yakai Alhaji bango, domin ko da alamu hakurin alhaji Buba ya kara inda ya yanke shawarar daukar wani mataki.

Daga karshe, hakurin Samuel akan Madam Gloria fa ya kare domin ko ya bukaci tattaro mishi duka kudin shi dake hannunta inda har yayi ikrarin hada ta da hukuma in kudin sa basu fito ba zuwa wani dan lokaci, ko ya zata karke tsakanin su.

Wadannan dama wasu sauran batutuwan na nan a cikin shirin dadin kowa sabon salo episode 87 da zaku iya saukewa ko kalla a tashar YouTube ta gidan talabijin din tashar Arewa24 dake kasa..

Dadin kowa sabon salo episode 87


Share this on:
 • 149
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  149
  Shares