Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

A cikin wannan shiri na dadin kowa sabon salo episode 89 zaku ga yadda wasu gurbatattun yan siyasa ke amfani da wasu miyagun matasa don tayar da zaune tsaye a lokutan zabe.

An wanke Hafsatu matar malam Musa tsohon soja daga zargin sata da ake yi mata, sai dai kuma da alamu ta dauko wani sabon salo mara kyau wanda ka iya haifar musu da rikici a gidan nasu.

Malam Ayuba mai gadi dai sai kara kaimi yake wajen neman auren Hannatu yar wajen Kamaye awon igiya, duk da kasancewar matarsa aminiyar matar Kamaye ce, ko yaya batun zai kasance.

Wadannan dama wasu sauran batutuwan na nan a cikin shirin dadin kowa sabon salo episode 89 wanda zaku iya saukewa daga tashar YouTube ta gidan talabijin din tashar Arewa24 dake kasa

Dadin Kowa Sabon Salo Episode 89


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •